logo

HAUSA

Sin: Bai Kamata ‘Yancin Fadin Albarkacin Baki Ya Zama Kafar Nuna Kiyyaya Ga Musulmai Ba

2024-03-16 16:00:04 CMG Hausa

Mataimakin jakadan dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce bai kamata a yi amfani da ‘yancin fadin albarkacin baki a matsayin wata kafa ta nuna kiyyaya ga musulmai ba, haka kuma bai zama dalilin gwamnatoci na kin daukar mataki ba.

Ya ce, kasar Sin na kira ga kasashe su rungumi dabi’ar kin amincewa da keta doka, da daukar kwararan matakan yaki da wariya da cin zarafin musulmai da haramta nuna kiyyaya saboda da addini ko imani, da kuma kawo karshen rashin hukunta masu laifi. 

Dai Bing ya kara da cewa, kasar Sin na goyon bayan tattaunawa da musaya tsakanin mabambantan al’ummu da mabiyan addinai, tana kuma adawa da nuna wariya ko bambanci ga wasu mutane ko addini da biyewa wani bangare game da sabanin ra’ayi tsakanin al’ummu da kuma nuna fifko kan wasu, yana mai cewa, Sin na goyon bayan daidaito da koyi da juna da tattaunawa da dunkulewar al’ummomi.

Ya ce, Sin na kira da a tabbatar da hakkin samun ci gaba ga kowa, a kuma kawar da tushen dake haifar da wariya da rashin hakuri, kamar talauci da raini da rashin daidato a fannin tattalin arziki, tare da inganta dunkulewa da daidaito wajen samun ci gaba. (Fa’iza Mustapha)