An fara kada kuri’u a babban zaben kasar Rasha
2024-03-15 11:17:13 CMG Hausa
Da misalin karfe 8 na safiyar yau Jumma’a ne aka bude tashoshin kada kuri’u a yankunan gabas mai nisa na kasar Rasha, wadanda suka hada da yankin Kamchatskaya, da yankin Chukotskiy mai cin gashin kansa da dai sauransu, wanda hakan ke nuna cewa an fara kada kuri’u a zaben shugaban kasa na shekarar 2024 a hukumance.
Bayanin da babban kwamitin zaben kasar Rasha ya fitar ya nuna cewa, ‘yan kasar kimanin miliyan 110 na da ikon zabe. Gwamnatin ta kafa tashoshin kada kuri’u sama da dubu 90 a wannan karo, wadanda za su bude rumfunan su tsakanin karfe 8 na safe zuwa 8 da dare, tun daga ranakun 15 zuwa 17 ga watan nan.
Akwai jimillar ‘yan takara 4 da za su fafata a zaben shugaban kasar na wannan karo, ciki har da shugaba mai ci Vladimir Putin, da dan jam’iyyar Liberal Democratic Leonid Slutsky, da na jam’iyyar kwaminis ta kasar Rasha Nikolai Kharitonov, da kuma dan takarar New People Party Vladislav Davankov.
Bisa tsarin zaben shugaban kasar Rasha, dan takarar da ya samu kuri’u fiye da kaso 50 bisa dari shi ne zai lashe zaben. Kuma babban kwamitin zaben kasar zai tabbatar da sakamakon zaben kafin ranar 28 ga watan Maris, sa’an nan, zai sanar da sakamakon zaben cikin kwanaki 3 bayan ya tabbatar da shi. (Maryam)