logo

HAUSA

An ayyana filin jirgin sama na Zanzibar a matsayin daya daga cikin mafiya inganci a Afirka

2024-03-15 11:18:59 CMG Hausa

Babban daraktan hukumar gudanarwar filin jirgin saman kasa da kasa na yankin Zanzibar dake kasar Tanzania Seif Abdalla Juma, ya ce ayyana filin jirgin saman Abeid Amani Karume dake Zanzibar, a matsayin mafi inganci a nahiyar Afirka, zai bunkasa jawo masu yawon bude ido zuwa tsibiran dake yankin.

Seif Abdalla Juma, ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, bayan da gamayyar kungiyar hukumomin lura da filayen jiragen sama ta kasa da kasa, ta baiwa filin jirgin saman na Abeid Amani Karume lambar yabo ta ingancin hidimomi ta shekarar bana.

Kungiyar dai na fatan aiwatar da matakai na dunkule tsarin ayyukan filayen jiragen sama, ta yadda za su dace da matsayin inganci na bai daya.

A cewar Juma, nasarar da filin jirgin saman ya samu na da alaka da matakai daban daban da gwamnati ke aiwatarwa, na jawo jari mai tsoka ga fannin sufurin jiragen sama.

Filin jirgin sama na Abeid Amani Karume shi kadai ne a Zanzibar, kuma kamfanin gine gine na Beijing Construction Engineering Group, daya daga manyan kamfanonin gine gine a kasar Sin ne ya gina sashen sa na 3. (Saminu Alhassan)