logo

HAUSA

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Ga Taron Kwamitin Kare Hakkin Bil Adama Na MDD Kan Hakkin Yara

2024-03-15 14:00:19 CGTN HAUSA

Jakadan dindindin na kasar Sin dake ofishin MDD na Geneva, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland, Chen Xu, ya gabatar da jawabi a madadin kasashe 80, yayin taron kwamitin kare hakkin Bil Adama na MDD karo na 55, game da yadda fasahar kwaikwayon hazikancin dan Adama ke taka rawa wajen kare hakkin yara.

A cikin jawabinsa, Chen Xu ya ce, fasahar kwaikwayon hazikancin dan Adam sabon dandali ne na raya harkokin dan Adam, kuma ya kamata a nace ga shawarwari da samun ci gaba da more basirar dake tattare da fasahar cikin hadin kai, don gaggauta daidaita harkoki a wannan bangare.

Jawabin da ya yi na kunshe da shawarwari uku. Na farko, amfani da fasahar kwaikwayon kazikancin dan Adam bisa sanya batun kare hakkin kananan yara a gaban komai. Na biyu, nacewa ga adalci da more wannan basira, wato kara hadin kai da tallafawa kasashe masu tasowa a bangaren kimiyya, da kuma more dabaru masu yakini. Na uku, kokarin kai wa ga matsaya daya tare da fahimtar bambance bambance, wato mutunta ikon mulki da shari’a da halaye da al’adu da tarihi da kuma addinai na sauran kasashe, yayin da ake gudanar da harkokin daidaita fasahar.

Jawabin da Chen Xu ya yi daya ne daga cikin jerin jawaban da Sin ta gabatarwa kwamitin kare hakkin bil Adam, game da rawar da fasahar za ta taka wajen tabbatar da hakkin wasu mutane na musamman. (Amina Xu)