logo

HAUSA

Jami’in Diplomasiyya Na Kasar Sin Na Ziyara A Isra’ila Dangane Da Rikicin Gaza

2024-03-15 19:47:50 CMG Hausa

Wang Kejian, jami’in diplomasiyya na kasar Sin ya kai ziyara Isra’ila a jiya Alhamis, domin tattaunawa da jami’an kula da harkokin wajen kasar, dangane da rikicin Gaza da kuma dangantakar kasashen biyu.

Ma’aikatar kula da harkokin wajen kasar Sin ce ta bayyana hakan a yau Jumma’a, inda ta ruwaito jami’in na kasar Sin na kira da a dakatar da bude wuta da rikice-rikice domin tabbatar da samar da agajin jin kai da kuma kare fararen hula yadda ya kamata yayin da rikicin ke ci gaba da wakana.

Ya kuma yi kira da a warware batun Palasdinu a siyasance bisa kafa ‘yantattun kasashe biyu domin samar da zaman lafiya da jituwa tsakanin Isra’ila da Palasdinu.

A nata bangare, Isra’ila ta bayyana matsayarta da kuma damuwarta kan batun rikicin na Gaza. (Fa’iza Mustapha)