Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa’adin aikin tawagar UNMISS a Sudan ta kudu
2024-03-15 09:46:51 CMG Hausa
Kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa’adin tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu ko UNMISS a takaice.
A jiya Alhamis ne daukacin mambobin kwamitin tsaron 15 suka amince da kudurin mai lamba 2726, wanda ya tanadi tsawaita wa’adin ayyukan tawagar ta UNMISS har zuwa ranar 30 ga watan Afrilun dake tafe, tare da baiwa tawagar izinin daukar dukkanin matakan da suka wajaba na cimma nasarar ayyukanta.
Ana sa ran tsawaita wa’adin ayyukan tawagar ta UNMISS, zai bayar da karin lokaci ga kwamitin tsaron MDDr na kara nazartar shirin Sudan ta kudu na gudanar da zabe, da tattauna yiwuwar fadada tsawaita wa’adin ayyukan tawagar, ciki har da samar da tallafin tsare tsaren gudanar da zabe a kasar. (Saminu Alhassan)