logo

HAUSA

An gudanar da taron kafa kamfanoni na kasa da kasa a Afirka ta Kudu

2024-03-14 11:34:00 CMG Hausa

An gudanar da taron kafa kamfanoni na kasa da kasa a birnin Cape Town dake Afirka ta Kudu a jiya Laraba, inda matsakaita da kananan kamfanoni da wasu da aka kafa ba da dadewa ba fiye da 1000, da kamfanonin zuba jari fiye da 150, da kuma masu gudanar da tsare-tsare daga kasashe 43 suka halarci taron.

Jigon taron shi ne “hade nahiyar Afirka”, ya kuma shafi batutuwa iri iri, kamar goyon baya, da kyautata kwarewar masu kafa kamfanoni na zuriya ta gaba, da makomar zuba jari ga kamfanoni dake da hadari, da yadda matsakaita da kananan kamfanoni za su saba da canzawar tsarin makamashi, da kuma yadda yankin cinikayya cikin ‘yanci na Afirka ya hade nahiyar Afirka.

A gun taron, babbar kasuwa, da kimmiya da fasahar makamashi maras gurbata muhalli da kasar Sin take da su, sun jawo hankulan kamfanoni da baki mahalarta. Masu kafa kamfanonin sun yi amanar cewa, Sin dake tsayawa tsayin daka kan bude kofarta, za ta kawo musu dammamaki da karfin samun ci gaba.

Habibatu Thani, wata ‘yar kasuwa ce a fannin samar da tufafi daga Najeriya, tana kuma ganin cewa, kamfanonin kasashen Afirka suna fuskantar babban matsin lambar takara a farko-farkon kafa su, kuma kasuwar Sin daya ce daga cikin kasuwanni mafi girma a dukkanin fadin duniya, wadda ta samar wa masu kafa kamfanoni manyan damammakin yin kasuwanci.

Bugu da kari, Kgosientsho Ramokgopa, shugaban hukumar kula da wutar lantarki a Afirka ta Kudu, shi ma ya yi nuni da cewa, Sin abokiyar cinikayya mai muhimmanci ce ta kasashen Afirka, inda yawan cinikayyar dake tsakanin bangarorin biyu take ta karuwa. (Safiyah Ma)