Ci gaban kasar Sin na ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya
2024-03-14 15:55:34 CMG Hausa
Bisa alkaluman bunkasar tattalin arzikin kasar Sin na shekarun baya bayan nan, da shaidun zahiri dake fitowa daga sassan hukumomin kasa da kasa, muna iya ganin yadda tattalin arzikin kasar Sin ya zamo muhimmin karfi dake ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya, matakin dake amfanar al’ummun kasar ta Sin, yake kuma yin tasiri mai kyau ga sauran sassan kasa da kasa.
Idan mun waiwayi baya, muna iya tuna irin gudummawar da kasar Sin ta baiwa duniya, yayin da ake shan fama da annobar COVID-19, ta hanyar samar da gudummawar kayayyakin yaki da cutar, da rigakafi, kana Sin ta aiwatar da matakan wanzar da safarar hajojin bukatar yau da kullum zuwa dukkanin sassan duniya, musamman a gabar da kamfanoni da dama a sauran sassan duniya suka gaza sauke wannan nauyi.
Masharhanta na ganin wadannan nasarori, da gudummawa da Sin ta baiwa duniya, ba kawai sun faru ne hakan ba, hasali ma hakan sakamako ne na aiwatar da kyawawan manufofi masu karko, karkashin hadin gwiwar gwamnati da bangaren al’ummun kasar da suka dukufa wajen aiki tukuru.
Ana iya ganin yadda Sin ke kara karfafa hadin gwiwar raya tattalin arziki, da cinikayya, tare da sauran sassan kasashen duniya, yayin da a hannu guda take daidaita tsara ayyukan cudanya tsakaninta da sauran rukunonin samar da ci gaba na duniya. Kaza lika, Sin ta yi fice wajen bunkasa zuba jari, da bude kasuwanninta ga sassan kasa da kasa.
A ganin kwararru, salon samar da ci gaba mai inganci da Sin ke aiwatarwa, da yaukaka hadin gwiwarta da sauran sassa, musamman ma kasashe masu tasowa, ya haifar da tarin alherai na cimma moriyar juna.
Karkashin manufofi daban daban na inganta hadin gwiwa, Sin ta zamo cibiyar raya harkokin tattalin arziki da zuba jari ta duniya, kana manufofinta na raya tattalin arziki sun yi tasirin gaske a fannin yaki da fatara, da aza tubulin gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama, aikin da masharhanta da dama ke ganin kyakkyawan misali ne, kuma darashi da ya kamata sauran sassan duniya su yi koyi da shi. (Saminu Alhassan)