logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye takunkumin kasarsa kan Nijar

2024-03-14 13:58:43 CMG Hausa

A ranar jiya Laraba 13 ga watan Maris din shekarar 2024, gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da matakin bude iyakokin sama da na kasa tsakanin kasarsa da Nijar, matakin da ake kallo a matsayin wani sabon babi na dangantakar moriyar juna da ke tsakanin kasashen biyu.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko da wannan rahoto.

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da kansa ne ya sanar a ranar jiya da bude iyakokin sararin samaniya da na kasa tsakanin Nijar da Najeriya, har ma da duk wasu shingaye da takunkumi da suka shafi kasar Nijar. Wannan mataki na shugaban tarayyar Najeriya ya biyo bayan sakamakon taron gaggawa na kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika na CEDEAO ko ECOWAS da ya gudana a birnin Abujan Najeriya na baya bayan nan, inda shugabanni da gwamnatocin gamayyyar yammacin Afrika suka dauki matakan janye takunkumin da suka kakabawa kasashen kungiyar AES da suka hada Mali, Burkina Faso da kuma Nijar. Tun biyo bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 a Nijar, kungiyar CEDEAO da kungiyar UEMOA suka sanya wa Nijar takunkumi, wanda a tsawon fiye da watanni 7 ya kawo mumunan tasiri ga kasar har ma ga al’umarta ta fuskar tattalin arziki musammun kan shige de fice al’umomi da dukiyoyinsu tsakanin kasashen biyu. Ya zuwa lokacin da nike kammala hada wannan rahoto, babu wata majiya mai magana da yawun gwamnatin Nijar da ta yi tsokaci kan wadannan kalamai na shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da sunan gwamnatin rikon kwarya ko da sunan kwamitin ceton kasa na CNSP.

Amma duk da haka, al’ummomin kasashen biyu na ganin abin alheri ne ga kasashen Nijar da Najeriya, na sake komawa cikin harkokin kasuwanci da na huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu. (Mamane Ada)