logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya lashin takobin ceton mutanen da aka sace ba tare da biya kudin fansa ba

2024-03-14 09:49:13 CMG Hausa

Wata sanarwa da aka fitar a hukumance a ranar Laraba ta ce, shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya dauki tsayuwar daka wajen kin biyan kudin fansa domin sako daliban makaranta da mata da aka sace kwanan nan.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya bayyana umarnin shugaban kasar a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ya jaddada bukatar hada karfi da karfe tsakanin hukumomin tsaro domin ceto wadanda lamarin ya shafa.

Ministan ya jaddada kudurin gwamnati na lalubo hanyoyi da za a bi tare da abokan huldar kasa da kasa yayin da ta yi watsi da yin sulhu da gungun ‘yan bindiga.

Tuni dai jami’an tsaro sun kaddamar da bincike tare da aikin ceto a matsayin martani ga hare-haren, tare da tabbaci daga Idris cewa, ana ci gaba da kokarin ganin an dawo da wadanda lamarin ya shafa lafiya. (Yahaya)