Rahoton MDD: Rashin daidaituwar ci gaba na barin kasashe mafi talauci a baya
2024-03-14 15:38:24 CMG Hausa
Wani sabon rahoton da hukumar raya kasashe ta MDD (UNDP) ta fitar a ranar Laraba ya ce, rashin daidaituwar ci gaba yana barin kasashe masu fama da talauci a baya, yana kara ta'azzara rashin daidaito, da kuma haifar da dambarwar siyasa a duniya.
Sakamakon shi ne "rashin ci gaba mai hadari" wanda dole ne a magance cikin gaggawa ta hanyar hadin gwiwa, a cewar rahoton ci gaban bil adama na 2023/24 (HDR), mai taken "Warware matsalar rashin ci gaba: Sake hadin kai a cikin duniya mai cike da rarrabuwa ". (Yahaya)