logo

HAUSA

Kalankuwar al’adun Afirka ta kayata gasar wasannin nahiyar da Ghana ke karbar bakunci

2024-03-14 15:32:15 CGTN HAUSA

Kalankuwar al’adun kasashen Afirka da aka gudanar, ta kayata gasar wasannin nahiyar karo na 13 da Ghana ke karbar bakunci. Yayin bikin bude gasar a birnin Accra a makon jiya, an gudanar da nune-nunen fasahohi da al’adun nahiyar ciki har da raye-raye, da kade-kade, da jerin gwanon masu nuna fasahohi, wadanda suka yi matukar nishadantar da ‘yan kallo.

A cewar mashirya gasar, daya daga cikin makasudin gasar shi ne yayata al’adu da akidun al’ummar nahiyar Afirka.

Game da hakan, Abdul Safana, jami’i a tawagar Najeriya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, "Na yi matukar jin dadin yadda bikin bude gasar ya gudana. Da wannan na tabbatar cewa an cimma makasudin gasar".

A nasa bangare, wani Basine mai sha’awar wasanni Li Wei, cewa ya yi ya gamsu da kwazon tawagogin da suka halarci gasar ta hanyar nuna fasahohin al’adun kasashen su yayin bikin bude gasar.

Li ya ce "Wasu tawagogin na sanye da tufafin gargajiya na kasashen su, wasu na nuna al’adu na raye-raye a filin wasa, wanda hakan ya baiwa baki ‘yan kasashen waje damar kara fahimtar al’adun Afirka".

Gasar nahiyar Afirka karo na 13 da Ghana ta karbi bakunci, ta zamo muhimmin dandali na yayata al’adu, da wasannin Afrika a kasar dake yammacin Afirka.

Gasar za ta gudana cikin kwanaki 15, ta kuma samu ‘yan wasa mahalarta sama da 4,000 daga sassan kasashen Afirka daban daban, wadanda za su fafata a rukunonin wasanni 29, ciki har da kungiyoyin kasashe 8 da za su wakilci nahiyar a gasar Olympic ta bana, wadda birnin Paris na kasar Faransa zai karbi bakunci.

Cavani ya haskaka a wasan da Boca Juniors ta doke Racing Club

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Boca Juniors ta Argentina Edinson Cavani, ya ci gaba da haskakawa a yayin da kungiyarsa ke taka rawar gani a gasar firimiyar Argentina.

Yayin wasan da kungiyoyin biyu suka buga a karshen mako, dan wasan  Boca Juniors Lucas Blondel ne ya fara jefa kwallon farko a ragar Racing Club. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma dan wasan tsakiya na Racing Club, dan asalin kasar Colombia Juan Fernando Quintero, ya farke kwallon da aka zura a ragar kungiyarsa, bayan da abokin wasan sa Maximiliano Salas ya bugo kwallo ta sama daga bangaren hagu.

Sai kwallon Racing Club ta 2, wadda dan wasan ta Quintero ya zurawa Adrian Martinez, shi kuma nan take ya sa ta a ragar Boca. To sai dai kuma ‘yan wasan Boca ba su yi kasa a gwiwa ba, inda suka ci gaba da matsawa ‘yan wasan Racing Club lamba, har ta kai mai tsaron gidan Racing Club din Nazareno Colombo ya jefa kwallo cikin ragarsa, lokacin da yake kokarin kawar da kwallon da Lautaro Blanco ke kokarin jefawa a ragar.

Bayan dan lokaci ana fafatawa ne kuma dan wasan Boca Cavani ya saka kwallo da ka, a ragar Racing Club, bayan da Blanco ya dago kwallon daga da’ira ta 6. Sai kuma kwallon Boca ta 4 wadda dan wasan ta Nicolas Valentini ya jefa a ragar Racing Club mintuna 9 kafin tashi daga wasan, daga kwallon da abokin wasan sa Kevin Zenon ya bugo. Da kuma hakan aka tashi Boca na da kwallo 4, Racing na da kwallo 2.

Da wannan nasara, Cavani mai shekaru 37 ya jefa kwallaye 4 a raga, a wasanni 2 da ya bugawa Boca, wanda hakan ya sa ake kallon sa a matsayin dan wasa da tauraruwarsa ke haskawa a firimiyar Argentina.

Yanzu haka Boca ta daga zuwa matsayi na 5 a rukunin B da maki 16 cikin wasanni 10, maki 4 ke nan kasa da mai jan ragamar rukunin wato kungiyar Godoy Cruz. Ita kuwa kungiyar Racing ta yi kasa zuwa matsayi na 8, bayan da ta sake yin asarar maki 2.

A sauran wasannin da aka buga kuwa, kulaflikan Godoy Cruz da Newell's Old Boys sun tashi kunnen doki da ci 1 da 1, sai Huracan da Argentinos Juniors da su ma suka tashi kunnen doki 1 da 1. A wasan Defensa y Justicia da Union Santa Fe kuwa, kungiyar Defensa y Justicia ce ta yi nasara da ci 2 da 1. Sai kuma kungiyar Talleres Cordoba wadda ta buge Atletico Tucuman da ci 4 da 1.

Ghana ta lashe lambobi 4 a gasar wasannin nahiyar Afirka da take karbar bakunci

‘Yan wasan tawagar kasar Ghana, wadda ita ce ke karbar bakuncin kasar wasannin Afirka karo na 13 dake gudana, sun lashe lambobin yabo 4 a wasannin daga nauyi, da linkaya a ranar Lahadi.

‘Yar wasan daga nauyi ta kasar Winnifred Ntumi, ta lashe lambar yabo ajin mata na gasar. Mai shekaru 21 da haihuwa, Ntumi ta lashe lambar zinari a gasar daga nauyin kilogiram 45, da kuma azurfa 2 a gasar daga nauyin kilogiram 49 guda biyu mabanbanta.

A dai wannan rana, dan wasan linkaya na kasar ta Ghana mai shekaru 23 a duniya Abeiku Jackson, ya lashe lambar azurfa a tseren linkayar mita 50 salon “butterfly”.

Mashirya gasar dai sun ce ya zuwa ranar Lahadi, kasashen dake kan gaba wajen samun yawan lambobin yabo a gasar sun hada da Masar, da Aljeriya, da Afirka ta kudu.