An fitar da takardar bayani game da ka’idojin rayuwar baki ‘yan kasashen waje a kasar Sin
2024-03-14 21:04:46 CMG Hausa
Rahotanni daga ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin sun nuna cewa, domin kawo sauki ga rayuwa da ayyukan da baki ‘yan kasashen waje ke gudanarwa a kasar Sin, a kwanan nan, wasu hukumomin kasar Sin sun tsara wata takardar bayani game da ka’idojin rayuwa da ayyukan baki ‘yan kasashen waje a kasar.