logo

HAUSA

Biden da Trump sun samu nasarar zama ‘yan takarar jam’iyyunsu

2024-03-13 14:57:14 CMG Hausa

Shugaban Amurka Joe Biden, da tsohon shugaban kasar Donald Trump, sun samu nasarar zama ‘yan takarar jam’iyyun su, gabanin babban zaben shekarar nan ta 2024 da kasar za ta gudanar a watan Nuwamba.

Rahotanni daga kafofin watsa labaran kasar na cewa, hakan zai haifar da fafatawa mai tsanani tsakanin abokan hamayyar biyu, dake neman sake darewa kujerar shugabancin Amurka.

Bayan lashe kuri’un Georgia, shugaba Biden ya lashe kuri’un wakilan jam’iyya 1,968 cikin jimillar kuri’u 3,934, kuma da wannan ya zama dan takarar jam’iyyar Democrat a babban zaben dake tafe. Kafofin watsa labaran Amurka sun yi hasashen Biden zai lashe zaben fidda gwani na Democrat, a jahohin Mississippi da birnin Washington.

A daya bangaren kuma, Trump ya zamo dan takarar jam’iyyar Republican, bayan da ya lashe kuri’un jihar Georgia, da Mississippi da Washington. (Saminu Alhassan)