logo

HAUSA

Mene Ne Ainihin Nufin Amurka Kan Philippines?

2024-03-13 22:13:42 CMG Hausa

Jiya Talata ne Gina Raimondo, ministar kasuwanci ta kasar Amurka ta bayyana a birnin Manila, fadar mulkin kasar Philippines cewa, Amurka za ta goyi bayan Philippines wajen ninka yawan masana’antun kera sassan na’urorin laturoni na semiconductor, a kokarin magance samun yawan masana’antun kera mattarar bayanai ta microchip a wasu sassan duniya. Kafin wannan kuma, ta sanar da cewa Amurka za ta zuba jarin dalar Amurka fiye da biliyan 1 a Philippines. Shin Amurka tana son taimakawa Philippines ne cikin sahihanci? Ko kuma ta tsara nata makarkashiya?

A shekarun baya-bayan nan, Amurka ba ta zuba jari da yawa a Philippines ba, inda ta kan zuba mata dalar Amurka biliyan 1 a ko wace shekara. Tun bayan kafuwar sabuwar gwamnatin Philippines a watan Yunin shekarar 2022 har zuwa yanzu, Amurka ta kara hada hannu da Philippines, a yunkurin aiwatar da manyan tsare-tsare a yankin tekun Indiya da Pasific. Amma ba ta kara zuba jari a Philippines ba. Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2023 da ta gabata, Amurka ta kasance kasa ta 6 a fannin zuba wa Philippines jari, tare da zuba mata dalar Amurka biliyan 1, yayin da Amurka ta zuba wa Thailand dalar Amurka biliyan 2.3. Abin da ya kamata a lura shi ne jimillar mutanen Philippines ta fi ta Thailand yawa har da miliyan 40.

A matsayin kasar da ba ta cikin nahiyar Asiya, Amurka tana son kara hada hannu da Philippines ne domin yin amfani da ita wajen yaki da kasar Sin da kuma takaita karfin kasar Sin. Alal misali, Amurka ta riga ta sa hannu sosai cikin batun tekun kudancin kasar Sin.

A bangaren Philippines kuma, shin ba ta san ainihin manufar Amurka ba ne? A’a, ta sani sarai, tana son yin amfani da karfin Amurka domin cimma burinta, wato hawan dutsen teku na Ren'ai Jiao da tsibirin Huangyan a kullum, da samun riba sakamakon yadda Amurka ta danne ci gaban kasar Sin ta fuskar mattarar bayanai ta microchip. Amma a karshe dai za ta rasa abin da ma can ba nata ba ne. (Tasallah Yuan)