Sin ta yi kira ga G20 da ta ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya
2024-03-13 10:39:36 CGTN HAUSA
Mataimakin wakilin dindindin na Sin dake MDD Dai Bing, ya yi jawabi a gun taron manema labaru na kungiyar G20 da aka gudanar a jiya, inda ya yi kira ga mambobin G20n da su taka rawar da ta dace, wajen hanzarta ci gaban tattalin arzikin duniya.
Dai Bing ya ce, Sin na fatan mambobin G20 za su kara hadin kai don ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai karfi da dorewa, kuma mai jurewar juna, da kuma cudanya bisa daidaito.
Ya ba da shawara cewa, da farko dai a mai da hadin kai gaban komai, kuma Sin na fatan bangarori masu ruwa da tsaki za su kara hadin gwiwa a fannin kawar da talauci, da samar da isashen hatsi, da yi watsi da ra’ayin nuna bambanci da sauransu, ta yadda za a fadada gudunmawar da ake bayarwa wajen tabbatar da ajandar samun bunkasuwa nan da shekarar 2030.
Na biyu ya ce a raya hadin kan tattalin arziki a manyan fannoni, wato ya kamata mambobin su daidaita manufofin tattalin arzikinsu a manyan fannoni, da ma kafa tsarin tsaron harkar hada-dadar kudi ta yanar gizo, da daukar matakan da suka dace don magance kalubalolin hada-hadar kudi. Na uku kuma, a bullo da boyayyen karfin tattalin arziki na yanar gizo. Wato kamata ya yi, mambobin su kara tuntubar juna ta bangaren yanar gizo a mataki mai kyau, don kawar da gibin dake tsakaninsu.
Daga karshe dai, a ci gaba da ingiza kwaskwarimar tattalin arzikin duniya baki daya. (Amina Xu)