Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta tsame hannunta daga bayar da tallafin wutan lantarki
2024-03-13 09:36:54 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, sannu a hankali za ta tsame hannunta daga ci gaba da bayar da tallafi a bangaren sha’anin wutan lantarki a kasar.
Ministan wutan lantarki na kasar Mr. Adabayo Adelabu ne ya tabbatar da hakan ga wani taron manema labarai, inda ya ce, gwamnati ta gaji da narkar da makudan kudade a bangaren duk kuwa da cewa ta jima da shigo da ’yan kasuwa cikin sha’anin samar da wutar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan wutan lantarki ya ce, an yi ta samun kiraye kiraye daga bangarori daban daban na gwamnatin tarayya da dakatar da ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki, inda ya ce ko da bankin ba da lamuni na duniya ya kasance cikin masu irin wadannan kiraye-kiraye, amma dai gwamnati ta ki amincewa.
Mr Bolaji Adelabo ya ci gaba da bayanin cewa, duk da kalubalen da bangaren wuta ke fuskanta a kasar, gwamnati dai ba za ta bari bangaren ya durkushe ba, a don haka nema ya bukaci ’yan kasar da su kara daurewa wajen biyan sabon farashin wuta da ake cajar su a halin yanzu, kafin lokacin da za a kai ga samun daidaiton farashi.
Ministan ya ce, zai yi wahala duba da bashin da gwamnatin tarayya ke bin kamfanonin gas ta iya ci gaba da bada tallafin wutar lantarki, amma dai tsarin zai ci gaba har zuwa wa’adin shekaru 3 masu zuwa.
“Tallafin gwamnati zai ci gaba har zuwa karshen wa’adi, to amma za mu rinka rage yawansa lokaci zuwa lokaci.” (Garba Abdullahi Bagwai)