logo

HAUSA

Yadda kasar Sin ke yunkurin bude kofa ga kasashen waje ta hanyar samar da hajoji da hidimomi masu inganci

2024-03-13 08:47:47 CMG Hausa

Duk da karuwar yunkurin kange tattalin arziki da kasashen yammancin duniya ke yi da kira da a raba gari da kasar Sin da babakere da danniya. kasar Sin ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta bude kofarta ga kasashen waje bisa matakai masu inganci don jawo jarin kasashen waje. Hakan ya sanya “taruka biyu” wato taron majalisar ba da shawara kan hankokin siyasa CPPCC da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC da aka kammala ranakun 10 da 11 ga wata bi da bi, suka mai da hankali akan bude kofa ga kasashen wajen ta hanyar samar da hajoji da hidimomi masu inganci, wanda ya jawo hankulan kwararru da masana da masu sa ido wadanda ke bibiyar yanayin tattalin arzikin duniya yayin da suka yabawa yunkurin kasar Sin na bude kofarta da ga kasashen waje da kara kwarin gwiwa game da tasirin tattalin arzikin Sin ga duniya da yunkurinta na samar da hajoji da hidimomi masu inganci ga kasashen duniya.

Shugaba Xi Jinping a cikin jawabinsa na bude taron NPC a ranar 5 ga wata ya ce, A sabon zamani, dole ne a samu ci gaba mai inganci. Kuma bunkasa sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko shi ne abu mai muhimmanci da ake bukata wajen kara inganta ci gaba. Kirkirar kimiyya da fasaha na da muhimmanci kwarai, yayin da ake kara inganta ci gaba, kuma samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba shi ne tushen ci gaba mai inganci. 

A yayin tarukan biyu, manazarta da masu sa ido a duniya sun yi bibiyar sanarwa game da manufofi da shawarwarin tattalin arziki don kara fahimtar hanyar da kasar Sin ke bi wajen bunkasa tattalin arzikinta ta hanyar samar da hajoji da hidimomi masu inganci. Sun ce kwarewar kasar Sin na kara zaburar da duniya, musamman kasashe masu tasowa, yayin da suka ce bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin yana tasiri mai kyau ga tattalin arzikin kasa da kasa, haka kuma sun bayyana kwarin gwiwa kan burin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, da samar da sabbin dabarun aiki ko karfin samar da hajoji da hidimomi masu inganci.  

Cavince Adhere, wani masani kan huldar kasa da kasa da ke zaune a kasar Kenya, ya yaba da yunkurin Sin na bude kofa ga kasashen waje inda ya ce, hakan ya zama abin sha'awa ga kasashe masu tasowa. Kuma "Manufar kasar ta ginu ne akan turbar zaman lafiya, da kyakkyawar niyya ga sauran kasashe, da kuma mai da hankali kan kyautata rayuwar bil'adama baki daya", wanda ya bayyana dalilin da ya sa kasar Sin ke more alfanun ci gabanta da sauran kasashen duniya.

Kasar Sin ta hanyar shirye-shiryenta kamar su shawarar “Ziri daya da Hanya” da BRICS da FOCAC ta ci gaba da raba kwarewarta da kasashe masu tasowa da ba da gudummawar fasahohi da albarkatun kudi da na kwadago. (Sanusi Chen, Mohemmed Yahaya, Saminu Alhassan)