logo

HAUSA

Kamfanin Huawei ya horas da matasa 241 a arewacin Uganda

2024-03-13 13:06:59 CMG Hausa

Katafaren kamfanin fasaha na kasar Sin Huawei, ya horas da matasan kasar Uganda su 241, a fannonin ilimin na’ura mai kwakwalwa, karkashin shirin sa na “DigiTruck”.

Wata sanarwa da kamfanin na Huawei ya fitar game da hakan, ta ce a wannan karo, wasu daga cikin matasan gundumar Alebtong ta arewacin kasar ne aka horas a tsawon makwanni 3, horon da ya kammala a ranar 7 ga watan nan na Maris.

Da yake tsokaci kan hakan, babban jami’in jam’iyyar NRM mai mulkin kasar Denis Obua, ya jinjinawa kwazon kamfanin na Huawei, bisa yadda ya aiwatar da shirin na “DigiTruck”, wanda ya yi daidai da manufar bunkasa ci gaban Uganda.

Shirin “DigiTruck”, na gudana ne ta hanyar amfani da motar tafi-da-gidan ka, mai kewaya sassan yankunan kasa, wadda ake mayarwa tamkar ajin makaranta, don koyawa matasa fasahohin amfani da na’ura mai kwakwalwa, kamar fasahohin cinikayya da bincike ta yanar gizo.

Kaza lika, horon bangare ne na shirin kamfanin Huawei mai lakabin  “TECH4ALL”, wanda aka tsara domin ingiza manufar samar da horo ga kowa a fannonin amfani da na’ura mai kwakwalwa, da wanzar da ci gaban hakan tsakanin sassan kasa da kasa.  (Saminu Alhassan)