logo

HAUSA

Sin na kalubalantar EU da ta nace ga matsayin tabbatar da tsaron duniya baki daya

2024-03-13 13:49:51 CGTN HAUSA

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ba da jawabi a taron kwamitin sulhun majalisar, wanda aka kira domin tattauna batun hadin kan majalisar kungiyar tarayyar Turai ta EU, inda ya kalubalanci EUn da ta nace ga matsayin tabbatar da tsaron duniya baki daya.

Ya ce, Sin na goyon bayan bangarorin biyu, da su yi hadin gwiwa karkashin ka’idoji, da manufofin tsarin mulkin MDD, ta yadda za su ba da karin gudummawar kiyaye zaman lafiya, da tsaron duniya, don amfanar al’ummar duniya, da tinkarar kalubalolin duniya cikin hadin kai.

Ya kuma kara da cewa, rikicin Ukraine kalubale mafi tsanani da EU ke fuskanta, don haka ake bukatar sulhuntawa da gudanar da shawarwari. EU a matsayinta na mai ruwa da tsaki, wadda muradunta na da alaka da batun, kamata ya yi ta kara samar da sharadi mai kyau na magance matsalar.

Ban da wannan kuma, ya ce, kalubalolin da Afrika ke fuskanta na kara karuwa, don haka Sin na fatan EU za ta sauke karin nauyin dake wuyanta, don baiwa nahiyar Afrika tallafin karfafa kwarewar raya kasa, da magance kalubaloli da ma samun ci gaba mai dorewa. (Amina Xu)