logo

HAUSA

Kungiyoyi masu zaman kansu na Sin suna taka rawar gani wajen ingiza manufofin kare hakkokin bil adama

2024-03-13 10:21:33 CMG Hausa

Wasu gungun kwararru daga kasar Sin, sun bayyana kungiyoyi masu zaman kansu dake kasar a matsayin muhimman ginshikai da suka taka rawar gani, wajen ingiza ci gaban manufofin kare hakkokin bil adama, da kyautata tsarin jagorancin duniya.

Kwararrun sun bayyana hakan ne a jiya Talata, a gefen taro na 55 na majalissar kare hakkin bil adama ta MDD, yayin taron da aka gudanar a birnin Geneva, mai lakabin "ingiza matakan kare hakkokin bil adama, da samar da ci gaba mai dorewa, karkashin hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kan su”.

A tsokacinta yayin taron, mataimakiyar babban sakataren wata kungiya mai rajin bunkasa fahimtar juna tsakanin sassan kasa da kasa ta kasar Sin Zhu Guijie, ta ce kungiyoyi masu zaman kansu na Sin, sun tallafa matuka wajen ingiza ci gaban manufofin kare hakkokin bil adama na Sin.

Ita ma Li Juan, mai bincike a cibiyar nazarin hakkokin bil adama ta jami’ar Central South ta kasar Sin, cewa ta yi kungiyoyi masu zaman kansu na Sin, suna da muhimmiyar rawa da suke takawa, a fannin kare hakkokin bil adama da samar da ci gaba mai dorewa. (Saminu Alhassan)