logo

HAUSA

Firaministan Isra’ila ya nanata kudurin ci gaba da gudanar da ayyukan soja a Rafah

2024-03-13 10:54:00 CMG Hausa

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya nanata a jiya Talata cewa, sojojin kasarsa za su ci gaba da inganta ayyukan soja a Rafah, wato birnin kudancin zirin Gaza.

Wata sanarwa da ofishin firaministan ya fitar a jiya, mai kunshe da jawabin zantawa da manema labarai, a taron da kwamitin harkokin jama’a na Amurka da Isra’ila, ta hakaito Netanyahu na cewa, dole ne Isra’ila ta kawar da sauran dakarun Hamas dake Rafah, don samun nasarar yakin da take yi, idan ba haka ba, Hamas za ta sake taruwa, kana za ta sake daukar makamai, da kuma sake mallakar zirin Gaza. (Safiyah Ma)