logo

HAUSA

Faraministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya tattauna tare da wata tawagar Amurka

2024-03-13 09:38:17 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, wata tawagar kasar Amurka na wani rangadin aiki da sada zumunta tare da hukumomin kasar Nijar, inda tawagar ta je fadar faraminista a ranar jiya Talata 12 ga watan Maris din shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Wata babbar tawaga ce ta gwamnatin kasar Amurka dake karkashin jagorancin mataimakiyar sakatare-janar na kasar Amurka kan harkokin wajen kasashen Afrika madam Molly Phee dake ziyarar aiki a kasar Nijar a cikin tsarin huldar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu. Ita dai wannan tawaga ta hada da dokta Celeste Wallander, mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka kan harkokin kasa da kasa, janar Micheal E. Langley, kwamandan din Africom, mista Skye Justice, mataimakin darekta kan harkokin kasashen yammacin Afrika. Wannan tawaga ta samu ganawa tare da faraministan kasar Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine a fadarsa dake birnin Yamai a ranar jiya Talata 12 ga watan Maris din shekarar 2024. Haka kuma, tawagar Amurkan ta samu wani zaman taro tare da takwararta ta kasar Nijar. Inda tawagogin biyu suka maida hankali a karkashin jagorancin faraminista, kuma ministan kudi Ali Mahaman Lamine Zeine, kan wasu muhiman batutuwan da suka hada da tsaro, huldar dangantaka, demokaradiyya, da sauransu. A yayin wannan tattaunawa akwai halartar jakadar kasar Amurka dake Nijar, madam Kathleen Fitz Gibbon da kuma ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare, mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP da kuma mambobin gwamnatin rikon kwarya.

Kasar Amurka dai na kokarin daidaita huldarta tare da sabbin hukumomin kasar Nijar na kwamitin ceton kasa na CNSP tun bayan juyin mulki da ya hanbarar da gwamnatin tsohon shugaban kasa Bazoum Mohamed a ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.