Xi ya tattauna harkokin kasa tare da wakilai da mambobin manyan taruka biyu na kasar Sin
2024-03-12 14:24:25 CMG Hausa
An gudanar da manyan taruka biyu na kasar Sin a watan nan na Maris. Kuma yayin taron, shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya tattauna game da harkokin kasa, da ci gaba tare da wakilai da mambobin manyan tarukan biyu na kasar Sin har sau uku.
A ranar 5 ga watan Maris, wato ranar da aka bude taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC karo na 14, tunanin “inganta sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, bisa yanayin da ake ciki”, wanda babban sakatare Xi Jinping ya gabatar ya jawo hankalin jama’a sosai.
A sabon zamani, dole ne a samu ci gaba mai inganci. Bunkasa sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko shi ne abu mai muhimmanci da ake bukata wajen inganta ci gaba mai inganci.
Kirkirar kimiyya da fasaha yana da muhimmanci kwarai, yayin da ake inganta ci gaba mai inganci. Babban sakatare ya taba jadadda cewa, kirkira za ta kawo kyakkyawar makoma. Yayin da ya tattauna harkokin kasa tare da wakilai da mambobi a shekarar bana, an sake ambatar kirkirar kimiyya da fasaha.
Samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba shi ne tushen ci gaba mai inganci. Xi ya bayyana wa mambobin fannin muhalli, da albarkatu da aka kara yi a taron CPPCC na wannan karo cewa, ya kamata a karfafa kiyaye muhallin halittu, da kuma ba da sabuwar gudummawa wajen kare ci gaba mai inganci ta hanyar babban mataki. (Safiyah Ma)