Guterres ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza da Sudan a Ramadan
2024-03-12 09:49:45 CMG Hausa
Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza da Sudan a cikin watan Ramadan a ranar Litinin.
Ya ce, a yayin da Litinin ta kasance ranar farko ta watan Ramadan wata mai tsarki, lokaci ne da al’ummar musulmi a fadin duniya ke gudanar da ibadu da yada dabi’un zaman lafiya da sulhu da hadin kai. Amma duk da haka ana ci gaba da kashe-kashe, da tashin bama-bamai da zubar da jini a Gaza.
Ya shaidawa manema labarai cewa, “Ina kira da babbar murya a yau cewa a girmama watan Ramadan ta hanyar tsagaita bude wuta da kuma kawar da duk wani cikas don tabbatar da isar da kayayyakin agajin ceton rayuka a cikin sauri kuma cikin adadi mai yawa da ake bukata”.
Guterres ya kara da cewa, “A Gaza da Sudan da ma sauran kasashe, lokaci ya yi a wanzar da zaman lafiya. Ina kira ga shugabannin siyasa da na addini da na al'umma a ko'ina da su yi duk abin da za su iya domin ganin wannan lokaci mai tsarki ya zama lokacin tausayawa da aiki da zaman lafiya.” (Yahaya)