logo

HAUSA

Wakiliyar CPPCC wadda take kokarin neman mafita ga sha’anin kiwon Reindeer

2024-03-12 14:05:49 CGTN HAUSA

DAGA MINA

Kabilar Ewenki dake zama a yankin Mongoliya ta gida na kasar Sin, an yi mata lakabin “Kabila ta karshe dake yin farauta a kasar Sin”, kuma rayuwar al’ummar kabilar ba ta rabuwa da dabbar Reindeer, dabbar da ta sha bamban da sauran dabobbi, sakamakon yadda Reindeer ke bukatar neman abinci a daji, ba za a iya kiwon su a gida ba. Du Mingyan, ‘yar kabilar Ewenki ce, kuma mamba ce a majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a takaice, wadda take kokarin neman mafita wajen kiyaye wannan dabba da taimakawa al’ummar wurin wajen samun arziki dangane da wannan sha’ani.

Sau tari ne malama Du Mingyan ta kai ziyarar bincike a sassan da al’ummar Ewenki ke rayuwa a birnin Hulunbuir dake yankin Mongliya ta gida, don fahimtar yanayin rayuwarsu. Bisa nazarin da take yi, ta gabatar da shawarwari da rahoto har 9 game da yadda za a raya ayyukan kiyaye Reindeer a wurin, kuma karkashin jagorancin hukumar wurin, an kafa yankin kiwon Reindeer na farko na kasar Sin a garin Aoluguya na ‘yan kabilar Ewenki da ke birnin Hulunbuir, an kuma gina wurin shakatawa bisa al’adun ‘yan kabilar Ewenki da ke shafar dabbar Reindeer, wanda ya samu matukar karbuwa daga baki masu yawon shakatawa.

An gudanar da taron shekara shekara na CPPCC a kwanan baya a nan birnin Beijing. A matsayinta na ‘yar majalisar CPPCC, Du Mingyan ta gabatar da shawararta, don neman sassan da abin ya shafa su samar da tallafi na manufofi, ta fannin kare dabbobin Reindeer daga cututtuka da kara haiyayyafarsu.

Du Mingyan daya ce daga cikin ‘yan majalisar CPPCC fiye da 2100 da suka fito daga bangarori 34 ciki har da tattalin arziki da al’adu da ba da ilmi da sauransu, wadanda suka hadu a wajen taron majalisar CPPCC don ba da shawarwarinsu game da yadda za a zamanintar da kasar Sin daga fannoni daban daban, don sauke nauyin dake wuyansu na ba da shawara kan harkokin siyasa da sa ido a fannin dimokuradiyya da tsoma baki cikin harkokin kasar.

Majalisar CPPCC na kunshe da wakilai daga jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sauran jam’iyyun demokuradiyya da ba na kwaminis ba, da wadanda ba sa cikin kowace jam’iyya, da rukunonin al’umma, da wakilai daga kananan kabilu da bangarori daban-daban, da wakilan ‘yan uwanmu daga Taiwan da Hong Kong da Macau, da wakilan Sinawa mazauna kasashen waje da suka dawo da dai sauran wasu bakin da aka ba su goron gayyata na musamman. (Mai zane da rubutu: MINA)