logo

HAUSA

Kasar Sin na taimakawa kasashen Afirka bunkasa sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko

2024-03-12 08:39:12 CMG Hausa

A cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin na shekarar 2024, an ce za a yi kokarin raya tsarin masana'antu na zamani a kasar, da gaggauta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko. Kana shugaban kasar Sin Xi Jinping shi ma ya jaddada bukatar aiwatar da manufar bisa yanayin da mabambantan yankuna suke ciki.

Dangane da hakan, wani shehun malami a tarayyar Najeriya mai suna Samson Ibion ya ce, ta la'akari da matsayin kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka samar da mafi yawan gudunmowa ga karuwar tattalin arzikin duniya, manufar da kasar ta dauka ta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, za ta amfani sauran kasashe masu tasowa. Lallai na yarda da ra'ayinsa.

Alal misali, aikin samar da motoci masu yin amfani da makamashi mai tsabta dake tasowa cikin sauri a kasar Sin, shi ma ya samar da damammaki na samun ci gaba a kasashen Afirka.

A wajen taron makamashi na nahiyar Afirka na shekarar 2024, wanda ya gudana a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu a kwanan baya, fasahohin kera motoci masu aiki da wutar lantarki na kasar Sin da aka nuna a wajen taron sun janyo hankalin dimbin kwararru na kasashen Afirka. Aminene Merwe, ita ce darektar kamfanin Green Cab mai fasahohin kare muhalli na kasar Afirka ta Kudu. Ta ce motocin wutar lantarki na kasar Sin suna da makoma mai haske a kasuwannin kasar Afirka ta Kudu, saboda a cewarta, idan an kwatanta da motoci na sauran kasashe, "motocin kasar Sin suna da fifiko, ta fuskar yawan motocin da ake sayarwa, da farashi, da inganci, gami da karfin baturansu. "

A lokaci guda, kamfanonin kasar Sin sun fara hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Habasha, don samar da motocin wutar lantarki a can. Kasancewar kasar Habasha ta samu isasshiyar wutar lantarki, ta hanyar samar da ita ta karfin ruwa, ya sa gwamnatin kasar ke sa ran ganin wata makoma mai haske game da aikin samar da motocin wutar lantarki a kasar, inda take taimakon raya bangaren ta hanyar samar da wasu manufofi na gatanci. A nasu bangare, kamfanonin kasar Sin sun samu yafuwar harajin kwastam na shigo da sassan mota da aka yi musu, ta hanyar kafa ma'aikatun hada sassan motoci a kasar Habasha. Lamarin da ya ba su damar rage kudin da ake kashewa wajen samar da motoci, da farashin motocin da ake samarwa, gami da raya masana'antu, da samar da karin guraben aikin yi a kasar.

Ta wadannan misalai za mu iya ganin cewa, da farko, yayin da kasar Sin ke kokarin neman raya sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko, ita ma ta kai shi kasashen Afirka. Na biyu shi ne, ingancin kayayyakin Sin, da farashinsu, da fasahohin kasar, da tsarinta na zuba jari, dukkansu sun dace da ainihin yanayin da ake ciki a kasashen Afirka. Wannan ya kasance dabarar da ake dauka ta raya harkoki bisa yanayi da muhalli da ake ciki.

Bari mu dauki wani batu da ya shafi aikin sadarwa a matsayin misali. Kamfanin tantance yanayin kasuwannin kimiyya da fasaha na kasa da kasa Canalys, ya gabatar da wasu alkaluma a kwanan baya, wadanda suka nuna cewa, kamfanin samar da wayoyin salula na Transsion na kasar Sin, ya sayar da wayoyin salula har miliyan 34 da dubu 500 a kasashen Afirka a shekarar 2023, adadin da ya kai rabin wayoyin da aka sayar da su a nahiyar. Ta haka, kamfanin ya zama wanda ya sayar da mafi yawan wayoyin salula a nahiyar Afirka.

To, ko me ya sa wayoyin salula na kamfanin ke samun karbuwa a kasuwannin Afirka? Dalilin shi ne yadda kamfanin ke mai da cikakken hankali kan bukatu na mutanen nahiyar Afirka. Wayoyin salula na kamfanin, suna da fifiko, wato da farko ya fi biyan bukatun al’umma bakaken fata wajen daukar hotuna. Na biyu, ana iya sanya katuna na SIM da yawa a cikin wayar salula guda. Na uku, wayoyin salular suna kunshe da tsarin sarrafawa na harsunan Afirka. Yayin da na hudu, suke da batura masu karfi da dorewa. Na biyar, a cikin wayoyin salular akwai APP mai kunshe da dimbin wakokin kasashen Afirka. Na shida shi ne, akwai wayoyin salula iri-iri da za a iya zaba, kana dukkansu na da inganci da araha. To, duk wadannan halaye ne na musamman da suka dace da bukatun mutanen kasashen Afirka, da muhallin wuraren zaman su, wadanda suka sa wayoyin salula kirar kamfanin ke samun karbuwa a kasashen Afirka.

A sa'i daya kuma, wannan kamfani na kasar Sin ya kafa cibiyoyin kirkire-kirkire, da masana'antu, da sassa masu kula da sayarwa, da samar da hidimomi, a kasashen Najeriya, da Kenya, da Habasha, da dai sauransu, ta yadda aka kai fasahar sadarwa ta zamani a nahiyar Afirka, da samar da guraben aikin yi da damammaki na raya kai ga matasan nahiyar.

To, duk wadannan misalai ne na yadda kasar Sin take kokarin raya masana'antun zamani da sabon karfin samar da hajoji, da hidimomi masu karko a kasashen Afirka, bisa yanayin da kasashen suke ciki.

Wani shehun malami mai suna Robert Gituru, wanda ke jami'ar fasahohin aikin noma ta Jomo Kenyatta ta kasar Kenya, yayin da yake hira da manema labaru a kwanakin baya, ya ce, bisa matsayinta na kasa dake kan hanyar tasowa, kasar Sin ta fi sauran sassa fahimtar kalubalolin da kasashen Afirka suke fuskanta, kana tana da dabarun warware matsaloli da za su biya bukatun kasashen Afirka.

A ganina, wannan shi ne dalilin da ya sa fasahohin kasar Sin, da manufofinta ke samun karbuwa, gami da samar da hakikanin gudunmowa a kasashen Afirka. (Bello Wang)