logo

HAUSA

AU da MDD za su yayata yaki da ta'addanci ta hanyar wasanni da al'adun Afirka

2024-03-12 10:48:19 CMG Hausa

Hukumar wasannin motsa jiki ta Tarayyar Afirka (AU) da ofishin yaki da ta'addanci na majalisar dinkin duniya (UNOCT) sun sanar da hadin gwiwarsu na yin amfani da wasanni da al'adun Afirka don dakile ta'addancin da tsattauran ra’ayi a ranar Litinin.

Hukumomin biyu sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka yi a gefen gasar wasannin Afrika karo na 13 da ake gudanarwa a Accra babban birnin Ghana.

Valerio de Divitiis, jami'in gudanar da shirye-shiryen wasanni na duniya na UNOCT, ya ce hadin gwiwar ya yi daidai da hangen nesa na dabarun yaki da ta'addanci na MDD wanda ke karfafa kasashe membobin su karfafa inganta tsaro a kusa da wuraren da ke da rauni, gami da taron wasanni.

Decius Chipande, jami’in gudanar da hukumar wasanni ta AU, ya amince da wasanni a matsayin ingantacciyar kafar yayata zaman lafiya a duniya, domin yana janye hankalin matasa daga shiga ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Chipande ya ce hukumar wasanni ta AU za ta aiwatar da shirin aikin da aka tsara tare da UNOCT a fadin Afirka. (Yahaya)