logo

HAUSA

Bangaren Sin: Ya kamata mambobin kwamitin sulhun MDD su tsaya tsayin daka kan ruhin hadin gwiwa

2024-03-12 13:38:25 CMG Hausa

Jagoran tawagar Sin dake MDD Dai Bing, ya jaddada bukatar da ake da ita, ta mambobin kwamitin sulhun MDD su tsaya tsayin daka kan ruhin hadin gwiwa. Dai Bing ya yi kiran cikin jawabinsa ga taron tattaunawa da kwamitin sulhun ya gudanar game da dabarun sanin makamar aiki a jiya Litinin.

Ya ce, kwamitin sulhu tsari ne mafi muhimmanci na tsaron rukunonin kasa da kasa, kuma mambobin kwamitin sulhun suna da nauyin musamman na inganta zaman lafiya, da tsaron kasa da kasa, don haka ya kamata su bi ka’i’doji, da tsarin dokokin MDD ya tanada, su mutunta juna, su tattauna da juna cikin daidaito, su kula da damuwar juna, da kuma inganta kwamitin sulhun, ta yadda zai iya ba da gudummawarsa yadda ya kamata.

Dai Bing ya bayyana cewa, wasu kasashe masu kujerun dindindin a MDD sun mallake kasashen dake gabatar da daftari game da yawancin batutuwa, kana wasu kasashen dake gabatar da daftari suna sanya ra’ayinsu sama da na sauran sassa, wanda hakan ke haifar da rikice-rikice da yawa.

Bangaren Sin ya dade da cewa, gabatar da daftari na nufin nauyi a maimakon fifiko. Don haka a dace kasashe dake gabatar da daftari su tsaya tsayin daka kan adalci, su saurari ra’a’yoyin bangarori daban daban, su yi kokarin tattara matsayar da aka cimma, a maimakon gudanar da ka’i’doji na daban, da kuma cimma makasudi ta amfani da hanyoyin siyasa. 

Jami’in ya ce bangaren Sin na ganin cewa, ya kamata a kara kyautata tsarin kasashe na shirya daftari, da ba da kwarin gwiwa ga kasashe marasa kujerun dindindin a MDD, wajen zama kasashe masu iya gabatar da daftari, musamman ma sanya mambobin kasashen Afirka su zama kasashen dake iya tsara daftari a kan batutuwan kasashen nahiyar Afirka. (Safiyah Ma)