logo

HAUSA

Kamfanin Sin na taimakawa Afirka ta Kudu wajen warware matsalar wutar lantarki

2024-03-12 15:19:51 CMG Hausa

A shekarun baya bayan nan, Afirka ta Kudu tana fuskantar kalubalen samar da wutar lantarki. A garin De Aar dake jahar Northern Cape ta Afirka ta Kudu, aikin samar da wutar lantarki ta iska na De Aar da wani kamfanin makamashi na kasar Sin ya kirkira, ba kawai ya kawar da matsalar karancin makamashi a wurin ba ne, har ma hakan ya sanya fasahohin kasar Sin zama wata hanya ta inganta ci gaban zamantakewa a wurin. A cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku yadda kamfanin Sin ke taimakawa Afirka ta Kudu wajen warware matsalar karancin makamashin wutar lantarki.