logo

HAUSA

An rufe taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14

2024-03-11 15:39:13 CMG Hausa

Yau da karfe 3 na yamma, an gudanar da bikin rufe taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ko NPC karo na 14. Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja, Xi Jinping, da sauran shugabannin jam’iyyar da na kasa sun shiga wurin taron don halartar bikin rufe taron.(Safiyah Ma)