logo

HAUSA

Nuryan Maimaiti na bayyana labarai kan kogunan dubban Buddah na Kezil

2024-03-11 16:09:26 CMG Hausa

Dubban Kogon Buddah na Kezil suna cikin tsaunin Mingwutag dake gundumar Baicheng ta jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin. An fara tono jerin kogon Kezil ne daga karshen karni na 3 zuwa farkon karni na 4, wanda ya kai tsawon kilomita 3. Akwai jimillar kogo 251 da kuma zane-zanen bango masu murabba'in mita 10000 a ciki.

Rukunin kogon Kezil kamar maganadisu ne dake jawo hankalin Nuryan Maimaiti sosai, a matsayinta na darektar sashen karbar baki na cibiyar nazarin kogo na Kezil ta jihar Xinjiang, ta riga ta shafe shekaru 6 tana aikin binciken rukunin kogon, inda ta bar sawunta a duk wuraren da suke, don gano tarihin mu'amala da cudanya tsakanin kabilu daban daban na jihar Xinjiang.

Kuqa, wanda aka fi sani da Kucina, shi ne zango na farko a kan hanyar siliki lokacin da aka fara yada al'adun addinin Buddah zuwa kasar Sin. Lokacin da aka gabatar da addinin Buddah zuwa Kuqa, ya kuma kawo dimbin gine-ginen addini, da sassaka da zane-zane, wanda ya haifar da dimbin rukunonin koguna a yankin Kucha. Daga cikin su, jerin kogon Kezil na iya wakiltar fasaha ta kogon Kucina, kuma su ne jerin kogon addinin Buddah da aka gada mafi dadewa, mafi girma, mafi yawan nau'o'i, kuma mafi tasiri a Yankunan Yamma, wato wurin da ake kira da gama gari ga jihar Xinjiang ta kasar Sin da tsakiyar Asiya.

A wannan lokaci, jihar Xinjiang tana da sanyi, kuma dusar kankara da yawa da kauri ta rufe tsaunin Mingwutag, jerin kogon Kezil suna a kan dutsen Mingwutag, kuma wata hanya mai lankwasa ce ta hada manya da kanana kogo tare.

A tunanin yawancin mutane, ba zai yiwu mutane su zabi bude ido a nan a lokacin sanyi mai tsanani kamar haka ba, amma a kasan tsaunin dusar kankara, akwai wasu mutane dake tafiya a kan hanyar zuwa jerin kogon, kuma wadda take tafiya a gaba don yin bayyani ga sauran mutane, ita ce Nuryan.

Nuryan ta bayyana cewa, “Wannan ba abin mamaki ba ne, akwai masu yawon bude ido da yawa a lokacin rani, don haka ba zai yiwu a zauna a cikin kogo na dogon lokaci ba. Saboda haka, wasu masu sha'awar kogo da suke da kwarewa a fannin, suna zabar yin ziyarar a lokacin hunturu, wato lokacin da mutane kadan ne ke yawon shakatawa a nan, ta hakan za su iya yin cudanya sosai da jagororin.”

Nuryan 'yar Kuqa ce, a shekarar 2017, ta yi mu’amala da al’adun Kucina bisa radin kanta, kuma irin al’adun sun burge ta matuka. A daidai wannan lokacin, cibiyar nazarin jerin kogon Kezil ta jihar Xinjiang tana kokarin daukar ma'aikata domin yada al'adun Kucina. A matsayinta na ma'aikaciyar gwamnati a ofishin gwamnatin gundumar Kuqa, ta mika takardar neman aikin ba tare da bata lokaci ba.

Wata kawarta ba ta fahimci dalilinta na yin hakan ba, ta kuma tambaye ta, ko ya cancanci ta bar aikinta mai kyau, ta tafi cikin duwatsu don binciken kogo? Nuryan ta amsa cewa, idan mutane da yawa za su iya fahimtar tarihi da al'adun Xinjiang ta hanyar kokarin ta, a ganin ta, ya dace!

A shekarar 2018, Nuryan ta shiga cibiyar nazarin kogo ta Kezil, kuma ta fara koyon ilmin nazarin kayayyakin tarihi daga karce.

Nuryan ta ce, “Da farko, na san wadannan haruffa, amma haruffan ba su gane ni ba.” Ta yi bayani kan wannan jimlar da ta fada cewa, wurin da kogon Kezil suke, shi ne mahaifar addinin Buddah na kasar Sin, tana iya furta wasu kalmomin Buddah, amma ba za ta iya fahimtar su ba.

Ban da wannan kuma, akwai zane-zanen bango iri-iri a cikin kogon. Haka kuma ana bukatar ta fahimci nau’ikan zane-zane, da abubuwan da suka shafa da ma tarihinsu. Ta nemo wasu litattafai irin na tarihi da addinin Buddah, kuma ta dukufa wajen karanta su.

Nuryan tana son koyon ilmi, kuma ta kware wajen neman dabarun karatu. A duk lokacin da ta yi nazari kan wani kogo, ta kan bi bayanan kwararru don gane shi a dukkan fannoni. Misali, lokacin da ake rubutu game da fadi da tsayin wani zanen bango, da abubuwan da ke cikin zanen, da kuma halin musamman na mutanen dake cikin zanen, ita da kanta ta tantance dukkan wadannan daga cikin bayyanai da abubuwan da ta gano a cikin wannan kogon.

Bisa tushen litattfai da bayyanai, da ma fahimtar da ta samu da kanta, tare kuma da takaitawa da aiki da ilimin da ta yi, ta samu sakamako mai kyau cikin sauri a fannin koyon ilimin kogo.

Kasar Sin tana da wadatar al’adun da suka shafi kogo, don zayyana bayanai daga sauran al'amura, Nuryan ba wai kawai ta koyi ilmi kan jerin Kezil ba, har ma da wasu shahararrun rukunonin kogo, ciki har da na Mogao dake Dunhuang, da Longmen, da dai sauran su.

A cewar Nuryan, “Wasu masu yawon bude ido da suka taba ziyatar sauran wasu kogo, su kan kwatanta su da kogon Kezil, idan ba mu da ilimi game da kogon dake sauran wasu wurare, ba za mu iya amsa tambayoyinsu yadda ya kamata ba.”

A duk lokacin da ta yi magana game da kogon Kezil, Nuryan ta kan yi magana ba tare da tsayawa ba: a lokacin da tsohuwar Kucina ta zama tashar kasuwanci da ta hada babban yankin Turai da Asiya da ma wata muhimmiyar tasha dake kan tsohuwar hanyar siliki ne aka kawo addinin Buddah zuwa kasar Sin.

Irin wadannan mu’amalar al’adu da musayar cinikayya ne ke sa kaimi ga cudanya tsakanin kabilu daban daban, wanda ya kai ga jihar Xinjiang, inda dukkanin kabilu ke rayuwa tare da samun ci gaba yadda ya kamata a yau.