logo

HAUSA

Shugaban tarayyar ya sake bayar da sabon umarnin ceto daliban da aka sace a jihar Kaduna

2024-03-11 10:13:00 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya ce, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da sabon umarni ga jami’an tsaron kasar kan su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ganin sun ceto daliban da ’yan bindiga suka sace a garin Kuriga dake jihar Kaduna.

Ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya ziyarci yankin da al’amarin ya faru domin gabatar da alhinin shugaban ga iyaye da ’yan uwan daliban. Ya ce, babu shakka shugaban kasa ya kadu sosai da samun wannan munanan labarai, kuma ba za a yi kasa a gwiwa ba har sai yaran sun sami ’yanci.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Bayan wata ganawar sirri da mataimakin shugaban kasar ya yi da shugabannin al’umma dake kauyen na Kuriga da iyayen yaran da aka sace da shugabannin hukumomin tsaro da kuma jami’an gwamnatin jihar ta Kaduna, Sanata Kashim Shettima ya ce, burin kowacce gwamnati shi ne tabbatar da tsaron lafiyar al’ummarta.

A lokacin da yake jawabi a gidan gwamnatin jihar ta Kaduna, mataimakin shugaban kasar ya ce, “Na zo jihar ta Kaduna ne a madadin shugaban kasa domin gabatar da jaje ga gwamnati da al’ummar jihar Kaduna bisa abin takaicin da ya faru na sace wadannan dalibai namu.”

A jawabinsa gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce, ya gamsu da matakan da jami’an tsaro suke dauka wajen ceto daliban da aka sace. (Garba Abdullahi Bagwai)