logo

HAUSA

AU ta yi Allah wadai da sace dalibai yara da mata a Najeriya

2024-03-11 10:19:35 CMG Hausa

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU Moussa Faki ya yi Allah wadai da sace dalibai yara da mata a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da daliban makaranta sama da 200 a garin Kuriga da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar Alhamis, wanda aka ce shi ne garkuwa da mutane mafi yawa da aka yi a makaranta a 'yan shekarun nan.

Da yake tofa albarkacin bakinsa game da sace daliban wanda ya biyo bayan harin 'yan bindiga a garin Kuriga, Faki ya ce, lamarin dai shi ne barazanar baya-bayan nan da ta'addanci da rashin tsaro ke haifarwa a Najeriya musamman da ma nahiyar Afirka baki daya.

Shugaban kungiyar mai mambobi 55 na kasashen Afirka ya kara yin kira da a gaggauta sakin yaran da matan da aka sace ba tare da wani sharadi ba. (Yahaya)