logo

HAUSA

Al’ummar musulmi a tarayyar Najeriya su tashi da Azumin Ramadan a yau Litinin

2024-03-11 10:14:24 CMG Hausa

Mai alfarma sarkin musulmi a tarayyar Najeriya Alhaji Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin watan Ramadan jiya Lahadi bayan karewar watan musulunci na Sha’aban.

A jawabin da ya gabatar ta kafofin yada labaran kasar, Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi umarnin tashi da Azumin Ramadan yau Litinin kamar yadda sharuddan addinin musulunci suka tanadar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Mai alfamar sarkin musulmi ya ce, bayan samun labarin ganin watan na Ramadan da yammacin jiya Lahadi a wasu sassan kasar, hakan ya kawo karshen watan Sha’aban wanda ya cika kwanaki 29 bayan hijirar Annabi Muhamamdu SAW na 1445.

“Mun samu rahoton tsaiwar wata daga shugabannin addini musulunci da kungiyoyi daban daban dake sassan Najeriya kuma mun gamsu da bayanansu, a sabo da haka ranar Litinin 11 ga watan Maris 2024 shi ne zai kasance ranar 1 ga watan Ramadan shekara ta 1445 bayan hijira.”

Daga karshen sarkin musulmin ya bukaci daukacin musulman kasar da su yi amfani da wannan mai alfarma wajen yin addu’o’i samun saukin rayuwa a kasar da kuma zaman lafiya a duniya baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)