logo

HAUSA

In Sa Ya Rika Dole Ya Yi Tozo: Kwarewar Kasar Sin Na Kara Zaburar Da Duniya

2024-03-11 17:31:08 CMG Hausa

“Taruka Biyu” wato taron majalisar ba da shawara kan hankokin siyasa CPPCC da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC da aka kammala a jiya Lahadi 10 da yau Litinin 11 ga wata, harkar ce ta cikin gidan kasar Sin, amma tasirin kasar Sin a duniya da barbashin bunkasar tattalin arzikinta da salonta na zamanintar da kasa da al’ummarta na shafar duniya baki daya musamman kasashe masu tasowa wanda ya zama abin nazari ga sauran kasashen duniya.

A yayin tarukan biyu, manazarta da masu sa ido a duniya sun yi bibiyar sanarwa game da manufofi da shawarwarin tattalin arziki don kara fahimtar hanyar da kasar Sin ke bi wajen bunkasa tattalin arziki da zamanintar da jama'a. Sun ce kwarewar kasar Sin na kara zaburar da duniya, musamman kasashe masu tasowa.

Nasarar kyautata zamantakewar kasar Sin na nufin zamanantar da dimbin jama'a, da wadata ga kowa da kowa, da raya kayayyakin tarihi da al'adu, da daidaito tsakanin bil'adama da yanayi, da samun ci gaba cikin lumana.

Hanyar da kasar Sin ta bi game da zamanantarwa ta samo asali ne daga "wayewar da take da ita." La’akari da bambance-bambance tsakanin salon zamanantarwa ta  kasar Sin da kuma hanyar da kasashen yammacin duniya ke bi wajen neman zamanantarwa, ya sanya Cavince Adhere, wani masani kan huldar kasa da kasa dake zaune a kasar Kenya, tabbatar da  cewa "hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin ta zama abin sha'awa ga kasashe masu tasowa," wadda ta ginu a kan turbar zaman lafiya, da kyakkyawar niyya ga sauran kasashe, da kuma mai da hankali kan kyautata rayuwar bil'adama baki daya, wanda ya bayyana dalilin da ya sa kasar Sin ke more fasahohin neman ci gabanta ga sauran kasashen duniya.

 A zahiri muna iya ganin musabbabin nasarar kasar Sin ta yadda take inganta zaman lafiya da ci gaba tare da darajta girman kasuwarta, da tsarin ilimi mai zurfi, da hada-hadar kasuwanci da siyasa, da kuma babbar kasuwar hada-hadar kudi, da kyautata yankunan cinikayya maras shinge tare da mai da hankali kan tallafawa tsarin fitar da kayayyaki daga kasuwar gida zuwa kasashen waje a matsayin muhimman abubuwan da ke cikin salon zamanantarwata.

Keith Bennett, wani mai ba da shawara kan huldar kasa da kasa dake Landan ya  bayyana cewa, "Duk da cewa zamanantarwa tsari ne na duniya da kuma buri na duniya, za ta iya daukar salo da kuma nau'i daban-daban." Amma zamanantarwa irin ta kasar Sin "tana wakiltar wani sabon abu ne" wato wani abu da za a iya ganinsa a matsayin zamanantarwa ta hakika kuma a zahirance, cikakke, mai daidaito da kuma dorewa.

Masana da masu bibiyar yanayin ci gaban duniya sun shaida yadda kasar Sin ke kokarin samar da damar zamanantar da duniya, ta hanyar raba kwarewarta da kasashe masu tasowa da ba da gudummawar fasahohi da albarkatun kudi da na kwadago, kuma tana hakan ne saboda ai “idan Sa ya rika dole ya yi tozo”. (Yahaya)