logo

HAUSA

CPPCC Ya Rufe Cikakken Taronsa Na Shekara-shekara

2024-03-10 15:15:27 CMG Hausa

Da safiyar yau Lahadi ne aka kaddamar da rufe zama na biyu na cikakken taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) karo na 14, wadda ke zaman majalisar koli dake tattauna batutuwan siyasa na kasar.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar sun halarci taron da aka yi a babban dakin taron jama’a dake nan birnin Beijing.

Yayin taron, an amince da kudurorin da suka shafi rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar CPPCC da rahoto kan yadda aka tafiyar da shawarwarin harkokin siyasa da masu bayar da shawara suka gabatar bayan taron shekarar da ta gabata da rahoton da ya nazarci yadda aka amince da sabbin shawarwari da kudurorin siyasa kan zaman na biyu na CPPCC karo na 14.

Tun bayan bude taron a ranar 4 ga wata, sama da mambobin majalisar CPPCC 2,000 daga bangarori 34 ne suka yi tattaunawa mai zurfi tare da cimma matsaya kan batutuwa da dama. Zuwa karfe 8 na yammacin ranar 5 ga wata, majalisar ta karbi shawarwarin da adadinsu ya kai 5,898. (Fa’iza Mustapha)