logo

HAUSA

Sanarwar kawancen masu kishin kasa domin ‘yancin kai na FPS kan halin da Nijar ke ciki ta fuskar al’umma, siyasa da tattalin arziki

2024-03-10 16:08:19 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, kusan watanni 8 bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, kawancen kungiyoyin fararen hula na kishin kasa domin ‘yancin kai na FPS ya fitar da wata sanarwa kan halin kasa ta fuskar tattalin arziki, siyasa da na al’umma, a yayin wani zaman taro a ranar jiya Asabar 9 ga watan Maris din shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

A dunkule, sanarwar ta ce: Wannan juyin mulki ya bayyana karara matsalolin da suka dabaibaye kasar Nijar, dalilin ‘yan kasa suka amincewa da nuna goyon baya ga sabbin hukumomi na ganin cewa sojojin sun zo a matsayin masu ceto.

Wannan goyon baya na ‘yan Nijar ga mambobin kwamitin ceton kasa na CNSP ya kasance wani babban tarihi a cikin zukatan al’ummar Nijar, musamman ma game da batun soke yarjejeniyar soja tare da Faransa, samar da wutar lantarki ga ‘yan Nijar duk da cire wutar lantarki daga Najeriya, rike hada hadar kudi duk da takunkumin kungiyar UEMOA.

Duk da wadannan matsaloli ‘yan Nijar sun tsaya tsayin daka domin jurewa wadannan takukumai na kungiyar CEDEAO da UEMOA da ma tarayyar Turai a tsawon watanni da dama, lamarin da ya janyo karancin magunguna, da wutar lantarki da karancin kudi.

Cikin kokowar tabbatar da ‘yancin kai, al’ummar Nijar ta fuskanci Faransa da sojojinta, CEDEAO da kuma takunkuminta, wannan kuma tare da taimakon goyon bayan ‘yan uwanta na kasashen Burkina Faso da Mali.

Haka kuma sanawar FPS ta yi kira ga sabbin hukumomi da suka kara rubanya kokari wajen yaki da ta’addanci musamman ma a yankin Tillabery da kuma yankin iyakoki 3, idan har yanzu al’umomi suke ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga. Haka kuma kungiyoyin fararen hular sun yi kira ga wata hadaka ta kasashen AES domin yaki da matsalar tsaro.

Sanarwar ta yi kira ga kwamitin sojojin CNSP da ya dauki sandar mulki wajen yaki da cin hanci da rashawa, da karbo dukiyar kasa da aka sata, ba tare da bata lokaci ba, da kuma duba halin da ‘yan kasa suke ciki domin kawo sauki gare su musamman ma cikin wannan lokaci.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.