Fahimtar Tsarin Demokuradiyyar Kasar Sin Ta Taruka Biyu Na Kasar
2024-03-10 16:44:33 CMG Hausa
Manyan taruka biyu na kasar Sin sun sa duniya ta fara tunanin “Shin mene ne ma’anar Demokuradiyya”. A ra’ayin babban editan mujallar “Dang Dai” ta kasar Argentina, Gustavo Ng, tsarin demokuradiyyar kasar Sin dake mayar da hankali kan jama’a ta kowacce fuska, ita ce Demokuradiyyar da jama’a suke amfana da ita. A cewarsa, manyan taruka biyu da ake gudanarwa shekara-shekara, wata muhimmiyar taga ce da duniya za ta iya lura tare da fahimtar tsarin demokuradiyya dake mayar da hankali kan jama’a ta kowacce fuska.
Sun Jie, mambar Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC daga Beijing, ta gabatar da wasu shawarwari a yayin tarukan biyu na bana, wadanda suke mayar da hankali kan inganta tsarin tallafin abinci ga wadanda suka manyanta da kara kyautata al’ummar dake mayar da hankali kan tsoffi. A bara, Sun Jie ta mika dubban takardun tambayoyi ga jama’a da gudanar da bincike a yankuna da kuma shirya tarukan karawa juna sani, domin tabbatar da shawararta ta bayyana ainihin matsalar dake akwai.
Kusan wakilai 3,000 na Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC da sama da mambobi 2,100 na Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC daga dukkan fadin kasar ne suka hadu a Beijing, tafe da muryoyin jama’a zuwa dandalin mafi muhimmanci domin a dama da su cikin ayyukan tattauna batutuwan kasa, da bayar da shawarwari domin ci gaban kasar, lamarin dake kara nunawa duniya irin kuzarin da tsarin demokuradiyyar kasar Sin ke da shi.
Demokuradiyya ba ado ba ne, bai kamata a rika amfani da ita kamar kayan ado ba, sai dai don ta warware matsalolin da jama’a suke fuskanta. Bisa kididdiga, a bara, sassa da dama na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, sun karbi shawarwari sama da 12,000 da aka gabatar yayin manyan tarukan biyu, kuma an kammala nazartarsu a kan lokaci. Sassan sun amince da kusan ra’ayoyi da shawarwari 4,700 da wakilan jama’a na majalisar NPC da mambobin majalisar CPPCC suka gabatar, tare da kaddamar da sama da matakai da manufofi fiye da 2,000 wadanda suka inganta ci gaban tattalin arziki da ma rayuwar jama’ar kasar.
Ta wadannan taruka 2, duniya za ta iya fahimtar tsarin demokuradiyya irin na kasar Sin da fahimtar fa’idojinsa da ma tsarin ci gaban kasar. (Fa’iza Mustapha)