logo

HAUSA

Zaunannen kwamitin majalisar CPPCC ya gudanar da taro

2024-03-09 22:02:26 CMG Hausa

Zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin(CPPCC) karo na 14, a yau Asabar ya gudanar da taronsa.

Wang Huning, shugaban majalisar ne ya jagoranci taron.

Taron ya amince da daftarin wasu takardu, yayin da ya yanke shawarar mika su ga zaman rufe taro na biyu na majalisar CPPCC karo na 14 don yin nazari. (Yahaya)