logo

HAUSA

Minista: Kasar Sin tana da kwarin gwiwa wajen kiyaye yanayin samar da aikin yi

2024-03-09 20:48:29 CMG Hausa

A yayin da ake ci gaba da karfafa da kuma inganta karfin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin, kasar tana da kwarin gwiwar kiyaye da daidaita yanayin samar da aikin yi, a cewar ministar albarkatun jama’a da tsaron zamantakewa na kasar Sin Wang Xiaoping a ranar Asabar din nan.

Wang ta bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a gefen zaman taro na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 (NPC) kan batutuwan da suka hada da ilimi, da samar da aikin yi, da tsaron zamantakewar jama’a, da gidaje, da kula da lafiya, da yaki da cuttutuka, a nan birnin Beijing.

Wang ta ce kasar za ta samar da matakan daidaita yanayi ga masu neman ayyukan yi da inganta rayuwar jama'a, kamar ci gaba da manufofin inshorar zamantakewar jama'a na musamman da tallafin kudi, da fadada hanyoyin samar da aikin yi ta hanyar tallafawa kanana da matsakaitan masana'antu. (Yahaya)