Sakataren tsaron Amurka ya amince da samun "kudin yaki" a fili
2024-03-09 21:14:59 CMG Hausa
Kwanan nan, sakataren tsaron Amurka Austin Lloyd Austin, ya bayyana a wani taro a fadar White House cewa, rikicin dake tsakanin Rasha da Ukraine ya kawo “babbar moriya” ga tattalin arzikin Amurka. Ma'aikata daga ko'ina cikin Amurka ne suka kera makaman da kasar ta yi jigilar su zuwa kasar Ukraine, kuma wadannan jarin sun kara fadada ma'aikatun Amurka tare da samar da guraben aikin yi ga ma'aikatan kasar. Har ila yau, ya fito fili ya bayyana cewa, goyon bayan da Amurka ke ba wa 'yan kasar Ukraine ya ba su damar ci gaba da shiga cikin rikicin, tare da amfanawa tattalin arzikin Amurka.
A wannan lokaci, mutane za su iya gani a fili cewa, "tayar da rikici - haifar da yaki – samun yawan kudi - karfafa mulkin mallaka" ita ce hanyar da kasar Amurke ke bi a matsayinta na "injin tayar da yaki". Rikicin Rasha da Ukraine wani lamari ne kawai na Amurka na "neman dukiya ta hanyar yaki" da ma "neman mulkin mallaka ta hanyar yaki".
Irin wannan matakin na nuna danniya ko babakere dake son samar da rikice-rikice a duniya ya cancanci kulawa sosai daga dukkan duniya. Wannan kuma yana gargadin mutane cewa, ta hanyar karfafa ikon tabbatar da adalci na kasa da kasa ne kawai za mu iya tinkarar "injin tayar da yaki" irin ta Amurka yadda ya kamata, da samar da karin tabbaci ga zaman lafiya da ci gaban duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)