logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya yi Allah wadai da sace wasu mutane a jahohin Borno da Kaduna

2024-03-09 15:18:20 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da sace wasu mutane a Borno da kuma dalibai `yan makaranta a jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasan ya fitar da yammacin jiya Juma`a 8 ga wata a birnin Abuja, shugaba Tinubu ya bayyana wadannan hare-hare biyu a matsayi hauka, inda ya bukaci jami`an tsaro da su gaggauta ceto mutanen tare kuma da kamo wadanda suka aikata laifukan da nufin zartar da hukunci akan su.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya ce manyan shugabannin tsaron kasar sun yi masa bayani aka tagwayen hare-haren, inda ya tabbatar da cewa ba zai taba bari iyalan wadanda aka sace su dade cikin jimami ba, wajibi duk inda  mutanen suke a ceto su ba tare da an taba lafiyar su ba.

Da yammacin jiya Juma’a shi ma gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya ziyarci garin Kuriga dake yankin karamar hukumar Chikun inda wasu `yan bindiga suka sace wasu daliban makarantar firamare da na sakandire.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai gwamnan na jihar Kaduna yace ya ziyarci yankin ne domin jajantawa iyalan daliban tare da tabbatar masu da kokarin da gwamnati ke yi na ceto su.

“Za mu yi aiki da shugabannin al`umma da sarakuna da kuma matasa domin tabbatar da ganin cewa cikin ikon Allah kowanne yaro ya dawo gida”

Adadin dalibai 187 ne aka sace daga makarantar sakandire, sai kuma 125 daga makarantar firamaren yankin na Kuriga, to amma a jiya Juma’a 25 daga cikin adadin sun samu tsira, ragowar 287 kuma suna hannun `yan bindiga.(Garba Abdullahi Bagwai)