logo

HAUSA

An yi taron dandalin tattaunawa tsakanin kwararrun Sin da Afirka a Tanzaniya

2024-03-09 20:04:35 CMG Hausa

Jiya Jumma’a 8 ga wata, an yi taro na 13 na dandalin tattaunawa tsakanin kwararrun Sin da kasashen Afirka dake karkashin tsarin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya. Dandalin, mai taken “matakan zahiri da Sin da Afirka suka dauka don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya”, wanda ya samu halartar jami’an gwamnatoci da kwararru da masana sama da 300 daga kasashe da dama.

Taron ya samu dimbin nasarori, inda kwararru da masana sama da 100 na Sin da Afirka suka bullo da matsaya da suka cimma dangane da zurfafa samar da ci gaba da hadin-gwiwar kasa da kasa na kwararrun Sin da Afirka, da yin kira ga kasa da kasa da su fadada hadin-gwiwa da samar da ci gaba, don zamanantar da kasashe daban-daban, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)