logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin a Nijar Jiang feng ya gana da ministan kasuwanci da na kiwon lafiya na kasar Nijar

2024-03-09 15:54:35 CMG Hausa

A ranar 7 ga wata, jakadan kasar Sin a Nijar Jiang Feng ya gana da ministan kasuwanci da masana’antu na Nijar Seydou Asman, inda bangarorin biyu suka yi tattaunawa mai zurfi kan hadin gwiwa a fannonin cinikayya da zuba jari.

Jiang Feng ya bayyana cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai kan raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya da Nijar, kuma a shirye take ta ci gaba da zurafafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin biyu, da ba da gudummawa ga shirin raya tattalin arzikin Nijar. Ana maraba da Nijar ta fadada fitar da kayayyakin amfanin gona masu fa’ida zuwa kasar Sin.

Har ila yau a wannan rana, Jiang Feng ya kuma gana da ministan lafiya, yawan jama'a da zamantakewa na Nijar Garba Hakimi. Inda Jiang Feng ya bayyana cewa, fannin kiwon lafiya wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwar Sin da Nijar bisa yadda ya kamata. Tun daga shekarar 1976, kasar Sin ta aike da tawagogin likitoci 23 zuwa kasar Nijar, suna aikin tantance cuta da jinya ga miliyoyin majinyatan Nijar, tare da horar da kwararrun likitocin Nijar da dama. (Yahaya)