logo

HAUSA

Da gaske ne an tilasta wa al’umma aiki a Xinjiang?

2024-03-09 22:22:50 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

“Zan so in ce muku, bisa abin da na gani da ido, zance na wai akwai ‘aikin ala tilas’ wajen noman auduga a Xinjiang karya ce.” Malam Akram Memtimin ne ya yi wannan furucin a yayin amsa tambayar manema labarai. Akram Memtimin dan kabilar Uygur ne da ya fito daga wani kauye da ke jihar Xinjiang, kuma dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ne, wanda yanzu haka ke halartar taron shekara shekara na majalisar a birnin Beijing, babban birnin kasar. Ya ce, da wuya ya fahimci me ya sa akwai kafofin yada labarai na kasashen yamma da suke yada labarai na wai “an tilasta wa dubun dubatar ‘yan kananan kabilu a jihar Xinjiang aikin tsintar auduga da hannu”. Ya ce, “auduga fari fat arzikinmu ne, ta hanyar noman auduga, mun samu kudin sayen mota da gidaje, mun ji dadin rayuwarmu, har akwai bukatar a tilasta mana yin hakan?”

Abin haka yake, al’umma a duk kasashen da suka fito, burinsu shi ne su samu kudi ta hanyar yin aiki, don jin dadin rayuwa. Amma hakan ya zama “aikin ala tilas” a bakin gungun ‘yan siyasa da kafofin yada labarai na Amurka da sauran kasashen yamma.

Ban da haka, Amurka ta kuma matsa wa wasu kamfanonin kasashen waje irinsu Volkswagen da BASF, da su dakatar da ayyukansu a Xinjiang, bisa dalili na wai akwai “aikin ala tilas”. A game da wannan, Dr. Björn Alpermann, wani masanin harkokin kasar Sin a jami’ar Würzburg ta kasar Jamus, ya yi gargadin cewa, babu tabbas dangane da zargin da aka yi na wai ana “aikin ala tilas”. An ce, Dr. Björn Alpermann ya gudanar da bincike dangane da zargin da aka yi na wai “ana tilasta wa ‘yan kabilar Uygur aiki”, amma ba tare da gano shaidu ba. Ya yi gargadin kada a bar alhakin kan kamfanoni masu alaka da jihar Xinjiang, har ma a sanya haramci kan jihar Xinjiang baki daya. Ya ce, “A ganina, hakan ya wuce gona da iri, wanda ka iya haifar da barna ga al’ummar yankin, a maimakon a ce an taimaka musu.”

Amma ita Amurka hakan ta yi. Tun watan Yunin shekarar 2022, gwamnatin Amurka ta fara gudanar da dokar wai “Hana Aikin Tilas Ga Al’ummar Uygur”, bisa ga dokar, ta hana shigar da kayayyakin da aka samar a jihar Xinjiang zuwa kasar. Amurka ta yi hakan ne bisa sunan kare “hakkin dan Adam”, amma a hakika, hakan ya haifar da rashin ayyukan yi tare da mayar da al’umma cikin kangin talauci da suka baro a baya, kuma burinta shi ne ta gurbata abubuwa a jihar Xinjiang, don cimma burin dakile ci gaban kasar Sin baki daya.

Na taba zuwa Xinjiang sau da dama. Amma wallahi ban taba gani da idona abin da aka ce wai “aikin tilas” ba, a maimakon haka, na ga yadda al’umma ‘yan kabilu daban daban ke rayuwa cikin walwala. Don haka, ina so in yi wa wadanda suka kirkiro karyar tambaya, shin al’ummar kabilar Uygur ba su da ‘yancin yin aiki? Jita-jitar da aka yada ta wai “aikin tilas”, a hakika tana tilasta musu barin aiki, wadda ta sa suka kasa sayar da kayayyakin da suka samar. To hakan na kiyaye hakkin su ne ko lalata hakkinsu?

A zahiri dai, saurin bunkasuwar kasar Sin cikin ‘yan shekarun baya ya sa wasu kasashe matukar damuwa, don haka suke iya kokarin hana bunkasuwar kasar. Amma dai kasar Sin tana da ‘yancin tabbatar da ci gabanta, zamanintar da kasar mai al’ummar biliyan 1.4 babban ci gaba ne ga dan Adam baki daya. Baya ga haka, bunkasuwar kasar Sin da ma kasuwarta mai matukar girma, suna samar da sabbin damammaki ga kasashe daban daban.

Kamar yadda Bahaushe kan ce, gani ya kori ji. Muna fatan ‘yan uwanmu na Afirka za ku samu damar ziyartar jihar Xinjiang. Sabo da duk wadanda suka taba zuwa jihar, sun tarar da cewa, abubuwan da suka gani da ido a jihar, sun bambanta da wadanda suka karanta a rahotannin kafofin yada labarai na kasashen yamma. (Lubabatu Lei)