Biyan diyya da gwamnatin Canada ta yi ya tabbatar da matsayin dan leken asiri na Michael Spavor, dan kasuwar kasar!
2024-03-09 15:33:13 CMG Hausa
Kafofin yada labaran kasar Canada a baya-bayan nan sun ba da labarin cewa, gwamnatin kasar ta cimma matsaya da Michael Spavor, wani dan kasuwan kasar da kasar Sin ta kama a baya, domin biyan “diyya” na daurin kusan shekaru uku da aka yi masa a gidan yari bisa zarginsa da laifin leken asiri a Sin. An bayyana cewa, bangarorin biyu sun daidaita akan dalar Canada miliyan 7 a sulhun karshe.
Tun lokacin da aka kama Michael Spavor a shekarar 2018, gwamnatin Canada ta yi ta yayata cewa “kasar Sin na tsere da shi ba bisa ka'ida ba", kuma a wannan karon za a iya cewa ta kunyata kanta.
A cikin 'yan shekarun nan, idan aka zo batun cece-kucen da Canada ke yi game da abin da ake kira "shirin leken asiri na kasar Sin" da kuma "Sin ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Canada," a bayyane ake iya cewa, ba sabon abu ba ne ga wasu 'yan siyasar Canada su rungumi tunanin yakin cacar baka da bin Amurka wajen kai wa kasar Sin hari.
Komai yawan karya da gwamnatin Canada ta yi, ba za ta taimaka ba. Abin da ya kamata ta yi shi ne mutunta gaskiya, dakatar da shafawa kasar Sin bakin fenti, da fahimtar kasar Sin daidai. Canada ta bi sahun Amurka kuma ba wai kawai ta rasa kwarjininta ba, har ma da magoyon bayanta na kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)