logo

HAUSA

Hukumomin sauraron korafe-korafen jama’a na kasar Sin sun lashi takobin samar da muhallin kasuwanci mai kiyaye doka

2024-03-08 13:10:21 CMG Hausa

Hukumomin sauraron korafe-korafen jama’a na kasar Sin sun bayyana kudurinsu na samar da muhallin kasuwanci dake kiyaye doka da oda da kawo karshen laifuffuka.

Wannan na kunshe ne cikin rahoton aiki da Shugaban hukumar koli ta sauraron korafe-korafen jama’a ta kasar Sin Ying Yong ya gabatar a yau Juma’a, ga taro na biyu na Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin karo na 14.

Rahoton ya nanata cewa ana tabbatar da adalci da bayar da kariya bisa doka ga harkokin kasuwanci daban-daban.

Da yake zayyana jadawalin aikinsa a bana, rahoton ya lashi takobin kawo karshen laifuffukan da suka shafi harkokin kudi domin inganta ci gaban bangaren hada-hadar kudi na kasar. (Fa’iza Mustapha)