logo

HAUSA

Majalissar dattawan Najeriya ta bukaci da a sake nazari a game da manufar samar da wuta na kasa

2024-03-08 11:39:40 CMG Hausa

Majalissar dattawan Najeriya ta kawo shawarar sake nazari a game da manufar gwamnati a kan sha’anin wutan lantarki da kuma shirin cefanar da bangaren ga ’yan kasuwa.

A zaman majalissar na ranar Alhamis 7 ga wata ’yan majalissar sun ce muddin ana son samun ci gaban masana’antu da kuma maganin kalubalen  rashin aikin yi to  wajibi ne sai kasa ta wadata da wutan lantarki.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

A lokacin da ya mike yake ba da gudummawarsa, mataimakin shugaban majalissar dattawan Sanata Barau Jibril ya ce, hakkin majalissar ne tabbatar da ganin Najeriya ta fita daga kalubalen rashin wadataccen wutar lantaki.

“Sabo da ba za mu taba gusawa da inci daya ba ga bunkasuwar masana’antu ba tare da muna da wuta ba, saboda haka wannan al’amari ne da za mu ci gaba da tattaunawa a kai har sai mun kai ga cimma buri.”

Shi kuwa Sanata Adams Oshiomole shaidawa zauren majalissar ya yi cewa, shi dai a ganinsa batun shigo da kamfanonin masu zaman kansu wajen sha’anin samar da wuta a Najeriya ba dabara ba ce, domin kuwa sau tari gwamnati na amfani da kudin al’umma wajen ceto irin wadannan kamfanoni idan sun fuskanci matsalar kudi, amma kuma duk da haka kuma su kan gaza samarwa ’yan kasa wutar da suke bukata.

A tasa gudummawar shugaban majalssar dattawan Sanata Godswill Akpabio cewa ya yi, “Ban ga dalilin da zai sanya wasu kasashe suna amfani da makamashin nukiliya wajen samar da wutan lantarki ba, mu kuma a ce wai ba mu da damar yin hakan, su fa tuni suka rigaya suka samu ci gaban masana’antu ta amfani kuma da makamashin nukiliya.”

Daga karshen zauren majalissar dattawan na tarayyar Najeriya ya tabbatarwa ’yan kasa cewa su kara nuna juriya da hakuri gwamnati na bakin kokarin kawo karshen matsalar karancin wuta a kasa baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)