logo

HAUSA

Akwai karin damammaki ga zuba jarin waje a kasar Sin

2024-03-08 22:04:28 CMG Hausa

Ta fuskar duniya baki daya, yawan masu sha'awar zuba jari ya yi kadan, don haka kasashe daban daban na kara kokarinsu na jawo hannun jari. Ta yaya kasar Sin ke jawo hankula da kuma amfani da jarin waje? Da yadda za a karfafa bude kofa? Rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin na bana ya ba da nasa amsar.

Daga fadada jerin sunayen masana'antu da ke karfafa gwiwar zuba jari daga kasashen waje, zuwa kara ba da tabbaci ga masu zuba jari na kasashen ketare a fannin hidima, da kyautata jin dadin ma'aikatan kasashen waje da ke zuwa kasar Sin domin yin aiki, da karatu, da kuma yawon bude ido, jerin hakikanan matakan da suka dace sun samar da sauki ga ‘yan kasuwa na kasashen ketare, kuma sun ba da garanti mai muhimmanci don saka hannun jari da gudanar da kasuwanci.

Baya ga haka, rahoton ya ba da shawarar ci gaba da rage sassan da a baya aka takaita wa baki zuba jari, da soke takunkumi kan samun damar saka hannun jarin waje a fannin masana'antu, da sassauta damar shiga kasuwa ga wasu masana'antun hidima, ciki har da na sadarwa da na kiwon lafiya.

Jarin waje wani muhimmin karfi ne wajen zamanantar da kasar Sin, me ya sa har yanzu kasuwannin kasar Sin ke samun tagomashi daga jarin waje a wannan halin da ake ciki a duniya na samun raguwar zuba jari a kasashen ketare?

Babban jari yana bin riba. Bisa kididdigar da hukumar kasar Sin ta yi, a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, yawan riba da ‘yan kasuwar waje suka samu daga zuba jari kai tsaye a kasar Sin ya kai kimanin kashi 9%, wanda ya kai wani babban matsayi a duniya. Ba abu mai wahala ba ne cewa, zabar kasar Sin ya haifar da riba mai yawa ga jarin waje, wanda hakan ya sa kasashen waje suke nuna babbar sha’awar zuba jari a kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)